Tsofaffin Ma’aikata a Jihar Bauchi Suna Fama da Kuncin Rayuwa.

GWAMNAN JIHAR BAUCHI BARRISTER M.A. ABUBAKAR

Tsofaffin ma’aikata da suka kai kimanin dubu shida a jihar Bauchi wadanda suka bar aiki ba tare da an biya su kudadensu na ladar barin aiki ba, sun shiga cikin mawuyacin hali, lamarin da ya kai wasu ga samun nakasa a jikin yayin da wasu kuma suka mutu saboda tsananin wahala.

Shugaban kungiyar tsofaffin ma’aikata na jihar Bauchi, Alhaji Habu Gar shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Mohammed a Bauchi. Yace tsofaffin ma’aikatan suna bin gwamnatin Bauchi bashin Naira biliyan ashirin da shida na kudadensu.

Shugaban kungiyar tsofaffin ma’aikatan ya kara da cewa sama da shekaru bakwai suke fafatikar neman a biya wadannan kudaden amma har yanzu basu shiga hannunsu ba. Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta fito ta yi musu bayani a kan halin da ake ciki kuma ta biya kudaden.

Sai dai a nasa bangare, babban sakataren hukumar tsare tsare na gwamnatin jihar Bauchi Alhaji Yahuza Adamu yace kasafin kudin wannan shekarar ya tanadi kudade da za'a biya wadanan kudaden.

Your browser doesn’t support HTML5

Bauchi Gratuity