Ko a cikin kwanakin nan ma an sami tashin boma bomai a wani sansanin yan gudun hijira na garin Dikko a jihar Borno, har aka sami asarar rayuka da dama.
To sai dai kuma don hana kara faruwa hakan yasa gwamnatin kasar sake daukar dabaru na tsaurara matakan tsaro a sansanonin. Hon Ibrahim Bafitul, wanda ke zama mataimaki na musammam ga shugaban Najeriya kan harkokin tsare tsare da ci gaba. Yace shugaban kasa yayi magana da shugabannin tsaro da basu izinin su duba dabaru na tantance shiga da fice a sansanonin yan gudun hijira.
Suma ‘yan Majalisar Kasa na nuna kaduwar sune game da salon kunar bakin waken da ake kaiwa, Sanata Abdul’aziz Nyako, dake zama shugaban kwamitin ayyuka na musammam a majalisar Dattawa, yayi kira ga mutanen da ke kai wannan hare hare na rashin Imani da su hakura su daina.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5