Tsaron Kasa Aikin Kowa Ne, Inji Daliban Arewa Maso Gabashin Najeriya

'yan gangamin neman a kubutar da daliban da aka sace a Najeriya

Tallafawa ya zama wajibi inji hadakar daliban shiyyar arewa maso gabashin Najeriya tun da dalibai ake kashewa, kuma su aka hana yin karatu

Hadakar kungiyoyin daliban shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ta ce matsalolin tsaron da suka addabi jahohin shiyyar sun fi karfin a tsurawa hukuma idanu a bar ta ita kadai.

A kan haka ne hadakar kungiyoyin daliban ta gudanar da wani taro a Jalingo, babban birnin jahar Taraba.

Cikin takaici, da nuna damuwa daliban su ka kudiri aniyar bayar da ta su gudunmowa. Daliban su ka ce idan ana so a shawo kan wannan bala'i dole sai an hada kai, sai an hada karfi da karfe.

Comrade Mohamed Auwal Jibril shi ne shugaban hadakar kungiyoyin dalibai a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Aikin tsaro ba na hukuma ba ne ita kadai, inji daliban arewa maso gabas.-3':48"

Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a jahohin Adamawa da Taraba, Ibrahim Abdulaziz ne ya hada wannan rahoto.