Tsarin Iyali Hanya Ce Da Za'a Magance Mutuwar Uwa Da Yara

Kungiyar bunkasa lammuran tsarin iyali tare da hadin gwiwar hukumar lafiya ta kasa, sun gudanar da wani taro kashi na biyar mai taken 'Kirkiro da tsarin da kowa zai ci gajiya.'

An gudanar da taron ne domin tattaunawa game da muhimancin tsarin iyali, da kuma musayar ra'ayi kan yadda za'a rage yawan mace-macen mata masu juna biyu a Najeriya.

Dr Amina Aminu Dorayi, dake aiki da ma'aikatar kiwon lafiya a Abuja, ta bayyana irin alfanun dake tattare da tsarin iyali musamman ma ga mata. A duk lokacin da akace mata da miji sun tsara haihuwarsu, za'a ga cewar 'ya'yan da suke haifa suna da wadatacciyar lafiya.

Za kuma a ga cewar ita kanta uwa zata dinga samun natsuwa da lafiya mai dorewa a jikinta, wanda idan ba don haka ba, jikinta zai dinga samun rauni kana tana iya kamuwa da wasu irin cututtuka da ka iya shafar lafiyar yaran.

Tun a shekara ta 2012 ne gwamnatin Najeriya tare da manyan masu ruwa da tsaki, suka fara aikin wayar da kan jama'a kan tsarin iyali don inganta lafiyar mata da ta yara.