Wannan cece ku ce dai ya samo asali ne daga wata kira da Majalisar Dokokin Najeriya ta yi na cewa a aike mata da shawarwari da za ta iya amfani da su wajen yi wa Kundin Tsarin Mulkin Kasa garambawul, to amma sai Kungiyar Dattawan Arewa, a ta bakin Darektan Mu'amala da Manema Labarai kuma Mai Magana da Yawun Kungiyar, Dr Hakeem Baba Ahmed ta yi tir da wannan kira, inda ta ce barnar kudi kawai za a yi domin tun 1999 ake amfani da kundin kasa ba tare da la'akari da gyare gyaren da ake yi mata ba.
Hakeem ya ce makudan kudaden da ake ware wa wajen gyaran kundi ya kamata a yi amfani da su wajen ciyar da mutanen da ke sansanin 'yan gudun hijra, sannan kuma a samar da tsaro domin su ne bukatu na yanzu, musamman a shiyyar Arewa.
Akan wannan batu ne Sanata mai wakiltar Kankiya, Ingawa da Kusada a Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Babba Kaita ya ce yana goyon bayan Kungiyar Dattawan Arewar dari bisa dari domin tun shekara 2011 da ya zo Majalisa ake gyaran Kundin tsarin mulki amma bai amfani 'yan kasa ba. Babba Kaita ya kara jadadda cewa a tara masu ruwa da tsaki a yi wa kasa gyara amma ta kuri'ar raba gardama.
A halin yanzu dai 'yan kasa sun zuba ido su ga yadda za ta kaya a daidai lokacin da Majalisar Kasa za ta fara gyarar Kundin tsarin mulkin, wanda ake amfani da shi tun daga 1999.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5