Jama’a assalama alaikum; mu na fata kun a nan kalau kamar yadda mu kea nan Washignton DC. Yau mu na tafe da kashi na uku na muhawarar da mu ke yi game da halin tsaka mai wuya da Fulani ke ciki a Najeriya. Kamar yadda mu ka fada a baya, Fulani na fuskantar zargi a bangare daya - na cewa su ne aka fi gani - ko kuma ake zarginsu da cewa su na tafka ta’asa ta sace sacen mutane, da tsayawa kan titi su na tare mutane su na karbar kudade. Amma a daya bangaren kuma, su ne ake tausaya wa saboda halin wahala da su ke ciki a wasu sassa na Najeriya, musamman kasashen Yarbawa.
To a babin na yau za mu duba ko shin biyan wasu bukatun Fulanin zai magance abin da ake fama da shi? Sannan kuma za mu ji amsar tambayar da ake yi na cewa shin shi Shugabannin arewacin Najeriya, kama daga shi Shugaban kasa zuwa gwamnoni, su na tallafa wa Fulani ko kuma sun su masu ido ne kawai a wadannan wahalhalun da su ke fuskanta? Yaya kuma shawarar Gwamna Ganduje cewa a taimaka ma Fulani su daina zuwa kudu?
A yi saurare lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5