Ofishin MDD na MINUSCA dake Jamhuruyar Afirka Ta Tsakiya yace zai kara tura karin soja zuwa Bangassou inda suka ce fararen hula na neman mafaka a masallatai da Wata Chocin Katolika Da kuma Asibitin kungiyar bada agaji ta Likitocin Kasa da Kasa.
Shugaban ofishin MINUSCA Chief Parfait Onanga-Anyanga ya fadawa Kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Al’amarin abin Allah wadai ne amma muna yin abinda duk ya kamata domin ganin mun sake kwato Bangassou.” Ya kara da cewa “Kananan Yara da aka saka alatilas aikin soji da ake tunanin a buge suna cikin wadanda suka kai harin.
A wata sanarwa da ya bada, Sakataren MDD Antonio Guterres ya bayar a jiya Lahadi, ya bayyana bacin ransa akan wannan harin da aka kai akan fararen hula da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya a Bangassou. Yace farmakin da aka kai kan sojan kiyaye zaman lafiyar na iya zama laifin yaki.
Shi kuma shugaban Kasar Afirka ta Tsakiya Faustin Touadera ya fada jiya Lahadi cewa yayi niyyar ya je Bangassou domin nuna goyon bayan a ga al’aummar da abin ya shafa.