Muryar Amurka ta bi sawun wasu matan da suke sana'ar a Damagaran amma basu yadda su ambaci sunayensu ba sai dai bada bayani.
Sun bayyana cewa suna anfani da diga ne su kwakwulo duwatsu kafin su fara fasasu. Kowace mace ta kan kashe sefa dari wurin sayen kayan kwakwulo da duwatsun amma kuma a wurin sayarwa ta kan samu sefa jaka guda ko fiye da haka kowace rana.
Suna samun masu sayen duwatsun da suka fasa. Da kudin da suka samu suke taimakawa iyalansu koda ma mazajensu basu sami komi ba da zasu kawo gida.
Akwai wata maman Maryam wadda take aikin tare da 'ya'yanta wai saboda hana yaran zaman banza.
Matan dake fasa duwatsun a cikin gidajensu suke yi. Da sun kawo kayan aiki gida sai su fara fasawa kana su fitar da abun da suka samu gaban gida domin masu saye.
Acewar wata daga cikinsu fasa duwatsu aiki ne na karfi amma babu yadda zasu yi saidai su daure domin a yaki talauci. Tace da masassara da ciwon jiki suke kwana. Idan sun samu wata sana'ar zasu canza. Amma kafin hakan ya faru zasu cigaba da yin sana'ar.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5