Rahotanni a kafofin yada labaran Amurka suka ce, a karkashin wannan sabuwar dokar, kasar Iraqi bata jerin kasashe da galibin al'umarsu musulmi ne da dokar ta wucin gadi kan shige da fice ta shafa ba.
A dokar ta farko da Mr. Trump ya sanyawa hanu ranar 27 ga watan Janairu, kasashen Iraqi da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan da Syria da Yemen ne dokar ta shafa.
A halin da ake ciki kuma, jami'an shige da fice na Amurka sun tsare wani magidanci da iayalansa su biyar da suka sauka a tshar jirgin sama dake Los Angeles, kan hanyarsu ta zuwa birnin Seattle inda zasu zauna.
Wata takardar kara da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta shigar gaban wata kotu a madadin mutumin da matarsa, da yara, ta bukaci kotun ta bada umarnin a sake su.