Shugaban Amurka Donald Trump, zai fito da sabuwar dokar da zata hana baki daga wasu kasashen 7 da galibin al'umarsu musulmi ne zuwa Amurka, sai dai wannan karon sabuwar dokar "za'a ingantata" kuma za'a aiwatar da ita ba tare da rudani da aka fuskanta tattare da dokar ta farko. Kamar yadda ministan tsaron cikin gidan Amurka John kelly yayi bayani.
WASHINGTON, DC —
Da yake magana a taron shekara-shekara kan harkokin tsaro da ake yi a Munich na Jamus, a lokacin da aka yi zaman tattaunawa, Kelly yace, wannan karon, dokar ba zata hana wadanda suka sami VISA ta zuwa aiki a Amurka, ko wadanda suke da katin izinin zama da ake kira "Green-Card" sake shiga Amurka ba.
Haka nan dokar wannan karon ba zata shafi wadanda tuni suke kan hanyar zuwa Amurka, ko tuni suke tashoshin shiga kasar, kamar yadda ya faru a baya ba.
Ana jin gwamnati zata fidda sabuwar dokar daga gobe Talata, kamar yadda kafofin yada labarai na Amurka suka bada rahoto, wanda shi shugaba Trump da kansa ya tabbatar da haka.