Trump Zai Fuskanci Matsala Idan Ya Hada Harkokin Kasuwancinsa da Na Gwamnati

Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump

Matasalar da ake kallon shugaban Amurka mai jira gado zai fuskanta shine cudanyar harkokin kasuwancinsa da shugabancin Amurka, misali,kamfanin jiragen saman fasinja na Qatar shekaru yanzu yana haya a benen nan inda nan ne ofishin shugaban na Amurka mai jiran gado yake.

Kamfanin na Qatar yana rigima da wasu kamfanonin jiragen fasinjan Amurka uku watau American, da Delta da kuma United, suna zargin cewa tallafin kudi na biliyoyin dala da gwamnatocin yankin Gulf suke baiwa kamfanonin jiragen fasinjan Qatar, da Emirates da kuma Etihad, yana baiwa kamfanonin damar su yiwa takwarorinsu na Amurkan zagon kasa, wanda yake barazana ga ayyukan ma'aikatansu dubu dari uku.

Bayan kama kafar da baiyi nasara ba da kamfanonin na Amurka suka yi ga gwamnatin Obama, yanzu suna kira ga sabuwar gwamnatin Trump mai jiran gado ta saurari kokensu. Burinsu shine takawa kamfanonin na yankin Gulf da suke bunkasa birki ta wajen hanasu izinin sauka a tasoshin Amurka.

A gabas ta tsakiya, harkokin kasuwancin Trump sun hada da wani katafaren ginin Trump Towers a birnin Istanbul, gandun wasan Golf a Dubai, da ake sa ran za'a bude badi,da kuma shirin gina jerin O'tel O'tel a hadaddiyar daular larabawa, da Qatar da kuma kasar Saudiyya.

Wannan takaddama tsakanin kamfanin jiragen saman daga yankin Gulf, da kuma muradun kasuwancin Trump yadda zasu ci karo da muradun gwamnatin Trump a ciki da wajen kasar.