Trump yace sakamakon kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a ya nuna "Musulmi masu yawa suna da matukar kiyayya," ga Amurkawa.
"Har sai mun gano kuma muka fahimci wannan matsala, da kuma irin hadari da barazanar da zasu haddasa, kasar mu ba zata ci gaba da fuskantar hare hare daga mutanen da babu abunda suka amanna da shi illa jihadi, kuma basu da tunani ko tsinkaya da kuma mutunta ran Bil'Adama.
Bakar magana kan musulmi ba wani sabon abu bane ga Donald Trump, wanda yayi kira ga gwamnati ta saka ido kan masallatai, kuma bai debe shawararsa ta farko na saka sunayen musulmi dake Amurka cikin wani kundi na musamman ba.
Kalaman na Mr. Trump sun zo ne kwana daya bayan da shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga Amurkawa kada suna kyama ga musulmi, lokacinda yake jawabi kan harin ta'addancin da aka kai garin San Bernadino a California.
Fadar White ta shugaban Amurka bata yi wata wata ba wajen yin Allah wadai da shwarar da Trump ya bayar, tana cewa "baki daya shawarar ta saba halayya da tunanin Amurkawa.