Trump Ya Yi Watsi Da Bukatar Gungun Masu Zanga-zanga

Shugaban Amurka Donald Trump, yayi watsi da zanga-zangar da ta barke kan yunkurinsa na wargaza inshoran kiwon lafiya wadda ya kasance daya daga cikin nasarorin da shugaba Obama ya samu zamanin mulkinsa.

Mr. Trump a magana da yayi ta shafinsa na Tweeter a daren Talata yace, "gungun mutane da suke nuna fushinsu a taro da wakilansu 'yan Republican a majalisa, a hakikanin gaskiya, kuma galibi, tsari ne na masu sassaucin ra'ayi. Abun takaici! inji Mr. Trump.

Fadar White House ta fada jiya Laraba cewa, shugaba Trump, zai gabatar da sabon kudurin da zai maye gurbin dokar inshorar kiwon lafiya da aka fi sani da lakabin 'Obamacare' cikin "makonni masu zuwa."

A lokacin hutun mako daya da 'yan majalisa suke yi, wakilai 'yan Republican masu yawa sun gamu da fushin 'yan mazabun su a tarurruka da suke yi, masu zanga zangar suna bayyana fushinsu kan yunkurin da wakilai 'yan Republican suke yi na shekara da shekaru na ganin sun rusa dokar inshorar kiwon lafiya da Obama ya zartas.

A halin da ake ciki kuma, kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a ya nuna farin jinin shugaban na Amurka ya tsaya kan kashi 40 cikin dari, mafi karancin goyon baya ga sabon shugaban kasa, duk da haka magoya bayan shugaba Trump suka ce duk da rudani a sabuwar gwamnatin- sun gamsu da aikin shugaban na Amurka yake yi.