"Wannan umurni na Shugaban kasa wani mataki ne mai muhimmanci wajen karfafa tsaron kasarmu," a cewar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson a wani taron manema labarai, inda ya shelanta sabon umurnin. Ya kara da cewa, "Kare Mutanen Amurka wani muhimmin nauyi ne da ya rataya wuyar Shugaban kasa."
Bullo da wannan sabon matakin tsaron, tamkar amsawa ce gwamnatin Trump ta yi cewa umurninta na farko, wanda ta bayar ran 27 ga watan Janairu, na tattare da kurakurai. To saidai ba a sani ko sabon umurnin zai gamsar da masu suka, wadanda ke ganin an auna hanin ne kan Musulmi.
A wani yinkuri na tabbatar da cewa umurnin hana shigowar ya aiwatu cikin sauki kuma bai fuskanci wani cikas na shari'a ba, sabon umurnin ya banbanta ta fannonin da dama da aka yi takaddama kansu a na farko.
Cikin banbance-banbancen da su ka fito fili har da tsame kasar Iraki daga cikin jerin kasashen da aka hanawa shigowa. Sabon umurnin ya hana shigowa daga Iran da Libiya da Somaliya da Sudan da Siriya da kuma Yemen.