Trump Ya Nemi Su Yi "Gajeruwar" Ganawa Da Kim

Lokacin da Trump da Kim suka hadu a farkon shekarar nan a watan Fabrairu

Shi dai Shugaba Kim bai ce komai ba dangane da wannan goron gayyata na na Trump, yayin da fadar gwamnatin Korea ta Kudu, ta ce, ba a cimma wata matsaya ba kan haduwar shugabannin biyu, inda ta ce tana fatan za a  ci gaba da tattaunawa

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce a shirye yake ya sake haduwa da takwaran aikinsa na Korea ta Arewa, Kim Jong Un, a yankin da babu dakaru, wanda ya raba Koriyoyi biyu, domin su gaisa.

Trump ya bayyana hakan ne a wani sakon Twitter da ya wallafa, gabanin ya sauka Korea ta Kudu a yau Asabar.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a gefen taron G20 na kasashen da suka fi karfin tattalin arziki a Japan, Trump ya ce haduwar ta su ba za ta wuce ta minti biyu ba.

Shi dai Shugaba Kim bai ce komai ba dangane da wannan goron gayyata na na Trump, yayin da fadar gwamnatin Korea ta Kudu, ta ce, ba a cimma wata matsaya ba kan haduwar shugabannin biyu, inda ta ce tana fatan za a ci gaba da tattaunawa.

Ana dai fatan, wata sabuwar ganawa tsakanin Trump da Kim, za ta taimaka wajen farfado da tattaunawar da ake yi kan batun nukiliyan kasra ta Korea ta Arewa.