Trump Ya Ja Kunnen Dakarun Venezuela, Ya Nemi Su Yi Watsi Da Maduro

Yayin da shugaba Trump ke jawabi ga 'yan kasar Venezuela mazauna Amurka a birnin Miami da ke jihar Florida, ranar 18 ga watan Fabrairu, 2019

Ya kuma gargadi sojojin Venezuela cewa muddun su ka barar da wannan dama ta ahuwa, “ba za ku sami gabar fita ku hau tudun mun tsira ba; ba mafita gare ku, kuma ba abin yi gare ku.” Trump ya kara da cewa, “Za ku yi asarar komai.”

A wani jawabin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ga masu ruwa da tsaki, ciki har da sojojin Venezuela, ya yi kiran da a kawo karshen tsarin mulkin gurguzu a kasar ta Venezuela.

Trump ya ce Amurka na neman a kafa sabuwar gwamnati a Venezuelar cikin lumana, to amma kuma, “ba za a kau da yiwuwar amfani da duk wani zabi ba.”

Trump, wanda ke Miami a lokacin, ya yi kira ga sojojin Venezuela da su yi watsi da duk wani umurni daga Shugaba Nicolas Maduro, su kuma amince da tayin ahuwar da Shugaban Majalisar Tarayyar kasar, Juan Guaido ya masu, wanda Guaidon shi ne kuma Amurka da wasu kasashe kimanin 50 su ka amince da shi a matsayin shugaban kasar.

Ya kuma gargadi sojojin Venezuela cewa muddun su ka barar da wannan dama ta ahuwa, “ba za ku sami gabar fita ku hau tudun mun tsira ba; ba mafita gare ku, kuma ba abin yi gare ku.” Trump ya kara da cewa, “Za ku yi asarar komai.”

Gabanin wannan jawabin da Trump ya yi ga al’ummomin Venezuela da Amurka, Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce, “Amurka na sane da inda jami’an sojin Venezuela da iyalansu su ka bobboye kudade a fadin duniyar nan.”