Trump Da Sauran Shugabannin Duniya Sun Hallara a Taron G7

Shugaban Amurka Donald Trump (hagu) da shugaban Faransa Emmanuel Macron (dama)

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tarbi takwaran aikinsa Trump da sauran shugabannin da ke halartar taron, inda daga baya suka yi wata liyafa ta kasaita.

Shugaban Amurka Donald Trump, na halartar taron kasashe bakwai da suka fi karfin tattalin arziki a duniya na G7 a birnin Biarritz da ke kasar Faransa.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya tarbi takwaran aikinsa Trump da sauran shugabannin da ke halartar taron, inda daga baya suka yi wata liyafa ta kasaita.

Liyafar ita ce ta biyu da shugabannin biyu suka yi a Biarritz, duk da cewa kwana guda da ya wuce, Trump ya yi barazanar saka haraji kan wata barasa da ake shiga da ita Amurka daga Faransan.

Yayin liyafar, shugabannin biyu sun kara jaddada aniyarsu ta yin aiki tare, yayin da suka zanta kan jerin batutuwa da suka shafi sauyin yanayi, yakin Libya da Syria da Korea ta Arewa da Ukraine da Iran da kuma yadda ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a yankin Sahel.