Trump: Bana Fatan Yaki Da Kasar Iran A Kowane Hali

Shugaba Trump ya na neman kasar Iran da ta “canza hali ta”

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce yana fatan Amurka ba za ta je yaki da Iran ba, a dai-dai lokacin da ake ci gaba da tada jijiyar wuya da gabas ta tsakiya, yayin da wani dan diflomasiyar kasar ya nuna rashin kwarin gwiwa a kan batun.

“Ba na wannan fatan” Trump ya ce game da tambayar da aka masa a kan yiwuwar rikici da Tehran, yayin da ya fara tattaunawa da shugaban kasar Swiss Ueli Maurer.

Amurka da Iran, basu da alakar diflomasiya da juna, amma kasar Switzerland na wakiltan Amurka a gabas ta tsakiya.

Sakataren ‘yan jaridan fadar shugaban kasar ta White House, Sarah Sanders ta maimaita wa manema labarai yau Alhamis cewar, Trump ya na neman Iran ta “canza hali” ta kuma daina hamaya da duk wani mumunar cin zarrafi daga kasar islama.