Trump Ba Zai Halarci Liyafar 'Yan Jarida Ba

Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai halarci liyafar 'yan Jarida da za a yi a fadar gwamnatin ba. Wannan mataki a ganin wasu wata alama dake nuna cewa ya na kokarin kare kansa daga zolayar da za’a yi masa a yayin liyafar.

Trump ya bayyana shirinsa na kauracewa liyarafar ne a shafinsa na twitter inda ya ce “ ba zan halarci liyafar 'yan jarida a Fadar White House ba a wannan shekarar, ina mai muku fatan alheri da kuma nishadi a wannan yammaci!”

Shugaba Trump dai ya kan halarci wannan liyafi a kowace shekara, amma kuma ya ki zuwa a bara.

Yayin wannan liyafa a bara wacce aka yi a zamanin tsohon shugaba kasa Barack Obama, ya nuna mamakinsa kan abinda ya hana babban dan takara ta jam'iyar Republican a wancan lokaci halartar liyafar.

Wannan taron wanda akan yi amfani da shi wajen tara gudunmuwar, ya kan hada da 'Yan siyasa da shahararrun mutane da kuma Shugaban kasa da uwargidansa.

Trump dai ya na takun saka da kafafen yada labarai, tun bayan da ya karbi mulki ya ke ta caccakar wasu daga cikin manya-manyan kafafen yada labarai inda ya zarge su da cewa suna yada labaran karya.