Trump Ba Zai Fasa Janye Sojin Amurka Daga Syria Ba

Syria inda aka kai hari

Fadar shugaban Amurka ta White House tace har yanzu shugaba Donald Trump na nan daram akan kudurinsa na janye sojan Amurka daga kasar Syria, duk da kalamin da shugaban Faransa, Emmanuel Macron yayi na cewa ya cusawa shugaban na Amurka ra’ayin kada ya janye sojojin.

Wata mai magana da yawun fadar, Sarah Huckabee tace matsayin Trump bai taba chanjawa akan wannan lamarin ba, don haka har yanzu yana nan akan shirinsa na janye sojan Amurka din daga Syria.

A jiya Lahadi ne dai shugaban Faransa Macron yake cewa “kwannaki goma bayanda Trump ya bayyana anniyarsa na janye sojan, Faransa ta neme shi da ya sauya shawarar, ya kyale sojan Amurka suci gaba da zama a Syria, kuma ya yarda.”

Sai dai kuma daga bisani shugaban na Faransa ya nemi ya gyara maganar tashi, inda yace kasashen nasu biyu na ci gaba da zama akan turbar ganin an murkushe mayakan ISIS don maido da zaman lafiya a Syria.

Kasar ta Faransa dai ta bi bayan Amurka da Ingila wajen kai farmaki akan Syria a ranar Assabar din shekaranjiya.