WASHINGTON, D.C. —
Ranar 3 ga watan Afrilu na shekara 2019, kungiyar kwallon kafa ta Tottenham za ta fara buga wasan Firimiya a sabon filin wasanta, a wasan da za suyi tsakanisu da Crystal Palace.
An gina sabon filin wasa ne akan zunzurutun kudi har fan biliyan dubu
daya, kwatankwacin rabin tiriliyan na kudin Najeriya.
'Yan kallo dubu 62,062 zasu samu wajan zama cikin sabon filin wasan, hakan ya sa ya kasan ce mafi girma a birnin Landon, kuma shine na biyu a gasar Firimiyar Ingila bayan Old Trafford na Manchester United.
Filin wasan na zamani wanda akan iya nade ciyawar filin domin a buga wasanni Rugby.
Kungiyar ta sanya hoton tauraron dan wasan gabanta dan kasar Ingila Harry Kane a jikin gilashin kofar shiga filin wasan.