Toshewar Hanyoyin Mota Ya Kawo Cikas Ga Aikin Ceto

Muguwar guguwa da ruwa sun hallaka mutane a Philipines

Yayin da al'ummar duniya ke kokarin kai agaji kasar Philipines, toshewar hanyoyin mota ya kawo wata babbar matsala.
A yayin da kasashen waje ke ci gaba da aikawa da kayan agaji zuwa kasar Philippines wadda mahaukaciyar guguwar teku mai tsananin karfi tattare da ruwan sama ta yi ma kaca-kaca, kungiyoyi sun ce tsananin tarkacen da ya toshe hanyoyin motar kasar yana kawo cikas ga ayyukan ceto da na rarraba agajin.

Kwanaki uku a bayan da mahaukaciyar guguwar teku mai suna Typhoon Haiyan ta hauro kan doron kasa, har yanzu hukumomin Philippines su na kokari ne ma su gano irin barnar da ta haddasa.

A wani gefe, jiragen sufurin kaya na sojojin Amurka tare da wata bataliyar sojojin kundumbala sun isa kasar ta Philippines domin taimakawa.

Wakilin Muryar Amurka a yankin arewa maso gabashin Asiya, Daniel Schearf, yace jiragen sama masu saukar ungulu sun fara jigilar kayayyakin abincin gaggawa, da ruwan sha da wasu kayan na masarufi da bukatun yau da kullum zuwa yankin tsakiyar Philippines wanda mahaukaciyar guguwar ta yi ma kaca-kaca, kwanaki uku bayan da ta ratsa ta yankin.

Ga Ibrahim Alfa Ahmed dauke da fassarar rahoton na Daniel Schearf.

Your browser doesn’t support HTML5

Toshewar Hanyoyin Mota Ya Kawo Cikas Ga Aikin Ceto - 3:41