Kamfanin Facebook ya bayyana cewar yana tsammanin wata manhaja, ta ba wasu damar ganin hotunan dake cikin wayoyi ko kwamfutocin mutane, kamfanin ya kiyasta kimanin mutane milliyan 7 matsalar ta shafa.
Kamfanin yace manhajar ta gurbata hanyoyin ajiyar bayanan jama’a na bayanan sirri, kimanin manhajoji 1,500 ne akayi amfani da su wajen shiga cikin bayanan sirrin jama'a na tsawon kwanki, tun daga ranar 12 ga watan Satunba.
Kamfanin yace “Ina mai baku hakuri da wannan matsalar” kamfanin ya wallafa wannan jawabin a shafinsa na yanar gizo, kuma ya dau alkawalin zai sanar da duk mutanen da abun ya shafa.
Ainihin manhajojin na aiki ne wajen bayyanar da duk wasu hotuna da mutun ya aika ko ya sakasu a shafinsa don wasu su gani, amma manhajar bata da hurumin bayyanar da hotunan mutane da basu bada damar a gani ba.
Manhajar ta wuce gona da iri, na ba mutane damar ganin wasu hotunan mutane da basu bukaci a gani ba, ko kuma wasu hotuna da mutun ya saka a shafin nasa da zummar ajiya.
Kamfanin yanzu haka yana kokarin ganin ya magance wannan matsalar, da kuma kokarin ganin hakan bai faruba a gaba.