Tinubu Zai Gabatar Da Kasafin Kudin 2025 Ga Majalisar Dokokin Najeriya A Gobe Talata

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan yayin zaman Majalisar.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da kudirin kasafin 2025 a gaban Majalisun Dokokin kasar a gobe Talata.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan yayin zaman Majalisar.

Kasafin na 2025 zai kasance cikakken kasafi na 2 da Shugaba Tinubu zai gabatarwa Majalisun Dokokin Najeriya tun bayan hawan kan karagar mulki a watan Mayun 2023.

A jawabinsa, Akpabio yace za’a fara gabatar da kasafin kudin din ne da misalin karfe 11 na safiya a zauren Majalisar Wakilai.

A ranar 3 ga watan Disamban da muke ciki, Majalisar Dattawan ta amince da dokar kashe kudade mai matsakaicin zango (MTEF) ta tsakanin 2025 zuwa 2027 da tadabarun sarrafa kudade(FSP) da jumlarsu ta kai Naira tiriliyan 47.9.