Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari A Matsayin Shugaban NNPCL

Mele Kyari, hagu, Shugaba Tinubu, dama (Tsohon Hoto: Facebook/Bola Tinubu)

A watan Yunin 2019, tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara nada Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPCL.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake nada Mele Kolo Kyari a matsayin shugaban kamfanin mai na Najeriya NNPCL.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litnin, Kakakin Tinubu, Ajuri Ngelale, ya ce nadin zai fara aiki daga ranar Juma’a 1 ga watan Disambar 2023.

A watan Yunin 2019 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara nada Kyari a matsayin shugaban kamfanin na NNPCL.

Shi ne ya gaji marigayi Maikanti Baru, wanda ya yi ritaya daga aiki kafin rasuwarsa.

Cikin sanarwar, Ngelale har ila yau ya ce Tinubu ya kafa kwamitin gudanarwar kamfanin wanda Cif Pius Akinyelure zai jagoranta a matsayin shugaban da ba na gudanarwa ba.