A cigaba da daukar matakai da sabuwar gwamnatin Najerita ke yi da zummar, abin da ta kira, kyautata makomar 'yan kasar, ta amince da dokar bayar da bashin dalibta ba tare da kudin ruwa ba
Abuja, Nigeria —
A wani mataki da sabuwar gwamnatin Najeriya ta ce na bukasa imili ne ta hanyar bayar da damarmaki ga dalibai masu niyyar shiga manyan makarantun Najeriya, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu (GCFR) ya rattaba hannu kan dokar bada bashi ga dalibai ba tare da kudin ruwa ba.
Kudirin dokar shi ne samar da sauki ga dalibai 'yan Najeriya don samun damar zuwa manyan makarantu daga Asusun Ilimi na Najeriya ba tare da kudin ruwa ba.
-Yusuf Aminu