Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin Dr. Olayemi Michael Cardoso a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar (5), har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da shi a cewar wata sanarwa da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar.
WASHINGTON DC —
Wannan umarni ya yi daidai da sashe na 8 (1) na dokar babban bankin Najeriya na shekarar 2007, wanda ya bai wa shugaban tarayyar Najeriya ikon nada gwamna da mataimakan gwamnoni hudu (4) a babban bankin kasar Najeriya (CBN), ko da ya ke sai majalisar dattawan tarayyar Najeriya ta tabbatar da hakan.
Bugu da kari, shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin mataimakan gwamnonin babban bankin Najeriya (CBN), na tsawon shekaru biyar (5), har sai majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da su, kamar yadda ta jera sunayensu a kasa:
(1) Mrs. Emem Nnana Usoro
(2) Malam Muhammad Sani Abdullahi Dattijo
(3) Malam Philip Ikeazor
(4) Dr. Bala M. Bello