Shugaban Kasar Najeriya Bola Tinubu ya nuna alhininsa bisa rasuwar Sheikh Abdul-Hafeez Aṣhamu Abou, Baba Adinni na Legas, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Zartarwa na Babban Masallacin Legas.
Legas, Najeriya —
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Laraba a Abuja, ta ce Shugaban na mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan Baba addinin da al’ummar Musulmi a Legas, da kuma gwamnatin jihar Legas kan wannan babban rashi.
Ngelale ya ce, Tinubu ya yi jinjina ga irin ayyuka da kuma sadaukarwar da Baba Adinnin wanda ya rasu yana da shekaru dari a duniya wajen cigaba al'umar Musulmi a jihar a Legas a lokacin da yake a raye.
Tinubu ya ce “Baba mutum ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa jama’a da addini hidima. Wanda tarihi ba zai manta da shi ba a cikin al'umma*
Shugaba Tinubu ya kuma yi addu'ar Allah Ubangiji Ya jikan Baba addinin Ya kuma sada shi da Aljannah Firdausi.