Tinubu Na Kokarin Mayar Da Najeriya Kasa Mai Jam'iyya Daya - Babachir Lawal

Babachir David Lawan

Sai dai fadar shugaban kasar ta Najeriya ta ce Babachir yana wadannan kalaman ne saboda har yanzu yana fama da takaicin nasarar da Tinubu ya samu a zaben da aka yi.

ABUJA, NIGERIA - Babachir na maida martani ne kan hukuncin kotu da ya soke zaben gwamnonin adawa uku da nada mukaman da yake ganin fifita wani yanki ne.

Babachir Lawal wanda shi ne jagoran kamfen din da ya sayawa Tinubu tikitin takara a APC kuma ya mara masa baya har ya lashe zaben fidda gwani, ya raba gari da Tinubu a wajen tsayar da dan takarar mataimakin shugaban kasa don rashin hada Musulmi da Kirista a tikitin kamar yadda aka saba gani.

Wasu ‘Yan Arewa

Babachir Lawal ya ce zagon kasa ga lamuran shari'a na iya kawo karar-tsaye ga muradun dimokradiyya.

Da ya juya kan yankin arewa, Babachir ya ce akwai bukatar gaggawa ta hada kan yankin don matukar rabuwar kawuna da aka samu.

Fadar Aso Rock ta musanta shisshigi a lamuran shari'a da nuna ya dace Babachir ya san mulki zabin Allah ne.

Wata kotun kararraki a Najeriya

Baya ga wata sanarwa daga mai ba wa shugaban shawara kan sadarwa Bayo Onanuga da ke kare Tinubu, mai taimakawa shugaban kan labaru Abdul'aziz Abdul'aziz ya ce da alamun nasarar Tinubu na kular da Babachir.

Hakika kotu dai a Najeriya tun sauke tsohon babban alkali Walter Knaku Onnoghen da gwamnatin Buhari ta yi a ke caccakar sashen shari'ar da matakai da suka sabawa hankali ko da yake, an ce shari'a sabanin hankali.

Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:

Your browser doesn’t support HTML5

Tinubu Na Yinkurin Jeff Najeriya A Mulkin Jam’iyyar Daya - Babachir Lawal.mp3