Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya gana da takwarar aikinsa na kasar Qatar a jiya Talata a Washington, makwanni uku bayan da Saudi da wasu kasashen Larabawa suka aza takunkunmin harkokin cinnikaiya da ta diplosiya a wannan kasar mai arzikin mai kawar da Amurka.
Ganawar Tillerson a ma’aikatar harkokin wajen Amurka da Sheikh Mohammed bin Abdulrahaman Al Thani ta zo ne wuni guda bayan Qatar tayi watsi da bukatun Saudiya da Bahrain Da Misra da kuma hadaddiyar daular kasashen Larabawa cewar kafin su cire takunkunmin da suka azawa wannan karamar kasa.
Kasashen Larabawan guda hudu sun ce ba zasu daidaita dangantar su da kasar ta Qatar ba, sai ta amince da dukkan bukatunsu goma sha uku, ciki har da yanke alaka da Iran kuma ta rufe gidan telbijin Al Jazeera da gwamnati kasar ke gudanarwa.