Tsohon dan wasan Arsenal, Thierry Henry, yace bai fahimci dalilin da yasa ba’a sa sunan Thomas Muller, a cikin jerin ‘yan wasa uku da suka fi shahara a wasan kwallo, a bana ba.
Muller na cikin ‘yan wasan Jamus, da suka ci kofin kwallon kafa na duniya da aka buga a wannan shekaran kuma ya taimakawa Bayern Munich tayi nasara a Jamus.
Henry, yace Muller, na cikin mutane ashirin da uku, da aka zana sunayensu wanda daga ciki aka zabi mutun uku daga karshe kuma ya kasance babu sunan sa.
Koda yake Henry, yace wadanda aka zaban sun cancanta, amma Muller, ma ya cancanta.
Ya kara da cewa Messi da Ronaldo, suna da ban mamaki saboda abun ban mamakin da suke yi a faggen wasa ya wuce hankalin mutane, shima Neuer ya cancanci kasancewa a cikin amma yace mai yasa ba’a tuna da Muller, ba.
Your browser doesn’t support HTML5