Tazarce: Ana Rigima Tsakanin Turkiyya Da Turai

  • Ibrahim Garba

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya

Yinkurin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin don shinfida tafarkin tazarce ya janyo takaddama tsakanin Turkiyya da Turai

Jiya Asabar an hana Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Mevlu Cavusoglu, sauka a kasar Netherlands, a cigaba da fuskantar adawa da Turkiyya ke yi, yayin da ta ke kampe a fadin kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai.

Shugaban Turkiyya Rajab Tayyip Erdogan ya yi matukar yin Allah wadai da al'amarin, ya na mai bayyana takwarorin Turkiyya na NATO din da "Gyauron 'yan Nazi" wanda shi ne karo na biyu da ya kwatanta kasashen Turai da kasashen Nazi a wannan satin.

"Lallai, wannan kalami ne mai cike da shirme," abin da Firaministan Netherland ya gaya ma manema labarai kenan jiya Asabar. Ya kara da cewa, "Na fahimci cewa sun fusata ne, amma wannan kalamin, lallai, ya zarce iyaka."

Jim kadan bayan wadannan kalaman, kafar labaran gwamnati ta Anadolu ta bayar da sanarwa cewa Ministar Iyali ta Turkiyy, Fatma Betul Sayan Kaya, wadda a halin yanzu ta ke Jamus, za ta je kasar ta Netherland ta mota, kodayake tuni aka soke harkokin da aka tsayar cewa za ta yi jawabai ciki.

Da dama daga cikin kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai na adawa da ziyarce-ziyarcen Ministocin Turkiyya, wadanda ke kampe gabanin kuri'ar raba gardama kan batun canza kundin tsarin mulkin Turkiyya. Turkiyya na kokari ne ta samu goyon baya daga miliyoyin 'yan Turkiyya da ke Turai saboda Shugaba Rajab Tayyip Erdogan ya samu karin iko, wanda zai sa ya kasance bisa gadon mulki har zuwa 2029.