Tawagar Super Falcons Ta Yi Bore a Faransa

'Yan wasan Super Falcons na Najeriya

Tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta Super Falcons, sun yi bore na zaman dirshan a otel din da aka sauke su, bayan da aka cire su a gasar cin kofin duniya ta mata a Faransa.

‘Yan wasan sun ki fita ne daga otel din ina suka ce sai an biya su alawus dinsu.

A karshen makon da ya gabata Jamus ta fidda Najeriya daga gasar bayan da ta lallasa ta da ci 3-0.

Su dai ‘yan wasan na Najeriya sun yi zargin cewa ba a biya su kudadensu na alawus da aka yi masu alkawari ba.

Rahotanni sun yi nuni da cewa ce ‘yan wasan na bin hukumar kwallon kafar kasar bashin alawus-alawus tun wadanda ba a biya su ba a wasannin da suka yi shekaru biyu da suka gabata da kasashen Gambia da Senegal.

Sannan sun yi zargin ba a biya su alawus-alawus na kwanaki biyar ba a wannan gasa da ake yi a Faransa.

Amma rahotonin baya-bayan nan, sun yi nuni da cewa tuni an sasanta da ‘yan wasan har ma sun kamo hanyarsu ta zuwa Najeriya inda ake sa ran za su iso a yau Litinin.