Tawagar Sani Zoro Ta Isa Damagaran, Jamhuriyar Nijar

Alhaji Sani Zoro shugaban kwamitin 'yan gudun hijira na majalisar wakilan Najeriya

Tawagar majalisar wakilan Najeriya da Muhammaed Sani Zoro ya jagoranta ta isa Damagaran da zummar lalubo bakin zaren rikicin dake yawan aukuwa tsakanin 'yan kasashen biyu a yankin Damagaran din

Ziyarar wani mataki ne na kawo karshen takaddamar da ta faru tsakanin mutanen Jobi dake bangaren Najeriya da kuma na Koli dake cikin Nijar.

Alhaji Sani Zoro yace sun yi kokarinsu a Najeriya amma takaddamar taki ci taki cinyewa dalili ke nan suka ziyarci Damagaran domin ganawa da mai martaba Sultan na Damagaran domin mutanen suna daularsa ne.

Sultan din yana sane da matsalar wai can baya ma ya taba daukan matakan warware takaddamar. A cikin irin fadace fadacen har wani dan asalin Najeriya ya rasa ransa. Bayan wannan an sake yin wani da yayi sanadiyar raunata wasu.

Alhaji Abubakar Sanda Sultan din Damagaran yace ya san da ita amma basu samu saduwa ba da mutanen Najeriya. Daga baya ne suka samu bayanai daga sarkin Gumel.

Yace ya bada tabbacin cewa da yaddar Allah za'a shawo kan matsalar saboda kowa hankalisa ya kwanta.

Alhaji Sani Zoro yace tuntuni suka gabatar da matsalar gaban ofishin jakadancin kasar Nijar dake Najeriya da majalisar wakilan Najeriya Haka ma akwai anniyar gabatar da maganar wa majalisar kungiyar kasashen yammacin Afirka.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Tawagar Sani Ta Isa Damagaran Jamhuriyar Nijar - 4' 48"