Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kano ta tsakiya a Sanata Musa Kwankwaso yana mai cewa matasan da basu da aikin yi ne ake anfani dasu wajen haddasa tashe tashen hankali.
Ya furta haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar mazabarsa ziyarar jajantawa da ban hakuri ga mazauna yankin da ke da Hausawa ‘yan asalin mazabarsa masu kasuwanci da noma da su ma na daga ckin jama’ar da tashe tashen hankulan ya rutsa da su.
Sanatan ya ce sun fahimci akwai tunanin da wasu al’umomin keyi cewa ana fifita wani bangare wajen rabon albarkatun kasa, batun da ya ce kamata ya yi gwamnatoci a dukan matakai su fito da tsari da zai tabbatar da daidaito da yin adalci.
Onarebul Barr,ister Bashir Mohammed dan majalisar dokokin jihar Taraba mai wakiltar yankin ya nuna takaicinsa da irin halin da yankin ya fada ciki a daidai lokacin da suke dakon ci gaba yanzu da gwamnatin jihar Taraba ta farfado da kanfanin noma da sarrafa gahawa yayin da gwamnatin tarayya ke shirin cigaba da aikin gina madatsar ruwa mai bada hasken wutar lantarki.
Shugabannin al’umma da na addinai inji mai martaba sarkin Mambila Dr, Shehu Audu Baju za su himmantu wajen dinke barakar da ta kunno kai da hada kan al’umominsu don maido da dawamammiyar zaman lafiya.
A saurari karin bayani a rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5