Gaisuwar ta'aziyar ta biyo bayan harin da 'yan ta'ada suka kai akan babban Masallacin Juma'a dake gaban fadar sarkin Kano yayin da aka tayar da kabarar sallar Juma'a.
Mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Muhammed Namadi Sambo yace gwamnatin Najeriya ta kadu matuka dangane da harin bam din. Ya yiwa wadanda suka rasu da wadanda suka jika addu'a. Ya roki Ubangiji ya kawar ma kasar masifar Boko Haram.
Ya shaidawa sarkin Kano cewa abun dake faruwa ya wuce siyasa. Yace a wurare da yawa ana cewa gwamnati ce take yi. Yace babu ruwan gwamnati dangane da abubuwan dake faruwa. Manufar gwamnati ce ta kare rayukan kowa da kowa da dukiyoyinsu. Zaman lafiya ake so domin a samu cigaba.
Namadi Sambo ya cigaba da cewa maganar harkar tsaro tana hannun 'yan arewa. Na farko, mai ba shugaban kasa shawara akan tsaro 'dan arewa ne daga Sokoto, wato Sambo Dasuki. Na biyu ministan tsaro shi ma dan arewa ne, Janaral Aliyu Gusau, mutumin Zamfara ne. Babban sifeton 'yansanda, Abba, 'dan arewa ne daga Jigawa. Duk wadannan mutanen musulmai ne. Kana ya ce shi kansa musulmi ne mutumin Zaria. Yace babu yadda za'a ce dukansu musulmai 'yan arewa zasu yadda a yi wani abun da ba daidai ba dangane da arewa.
Ya roki sarkin Kano ya yi taimako a jawo hankalin mutane domin a samu hadin kai. Yace idan Allah ya yadda zasu kawo karshen wannan mummunan abun da Boko Haram ta kawowa kasar musamman arewa.
Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammed Lamido Sanusi II ya mayar da jawabi. Yace babu abun da zai faru sai Allah ya yadda. Mutanen da suka rasa rayukansu da wadanda suka jikata 'ya'yansu ne kuma suna cikin ibada aka hallakasu. Yayi fatan Allah ya karbi shahadarsu. Ya ja kunnuwan mutane kada su yi aiki da jita-jita amma su hada hannu da jami'an tsaro domin samun kwanciyar hankali. Ba'a fuskantar masifa da fushi amma da hakuri da dangana ga Allah.
Idan irin wannan ta'asa ta faru mai martaba yace ana bukatan shugabanni su bincika su gano yadda aka yi hakan ta faru. Su wanene suka aikata ta'asar. Wadanne hanyoyi za'a dauka saboda kare na gaba. Kana mutanen da abun ya shafa da kasashen da suka shafa menene hukuma zata yi ta taimaka masu. Wannan ne nauyin da Allah ya dora masu na shugabancin jama'a. Ya kira shugabannin kasa su karfafa tsaron kasar gaba daya. Sarkin ya godewa jami'an tsaron Kano. Yace suna iyakacin kokarinsu. Ya kira al'umma su taimaka su karfafa tsaro saboda abun ya fi karfin mutum daya ko wata hukuma daya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5