Tawagar Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Ziyarci Afirka ta Kudu

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara

Biyo bayan yadda 'yan Afirka ta Kudu ke farma baki musamman 'yan Najeriya suna kashesu suna wawure dukiyoyinsu, Majalisar Wakilan Najeriya ta yanke shawarar tura tawagarta zuwa Afirka ta Kudu domin ganawa da majalisar dokokin kasar inda za ta bayyana masu rashin jin dadin Najeriya bisa abubuwan da ake yi wa 'yan kasarta.

Manufar aikawa da tawagar ta Majalisar Wakilan Najeriya ita ce yadda za'a gano hanyar kawo karshen kyama da 'yan Afirka ta Kudu ke nuna wa 'yan Najeriya da sauran baki dake zaune a kasar.

Tawagar da ta hada da 'yan kwamitin harkokin wajen Najeriya da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje sun ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen kuntata wa 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu.

Kuma aikin 'yan majalisar ne su nunawa duniya cewa 'yan Najeriya na da gata.

Tawagar ta Najeriya za ta bukaci majalisar Afirka ta Kudu ta samu dokokin da za su hana sake aukuwar farma baki a kasar ta Afirka ta Kudu.

Za kuma su nunawa 'yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu cewa cin mutuncin 'yan Najeriya a kasarsu ya isa haka.

Ga rahoton Sale Shehu Ashaka da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tawagar Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Ziyarci Afirka ta Kudu - 2' 48"