A jiya Talata, wata tawagar sanatoci daga Majalisar Dattawan Amurka da aka aike zuwa Myanmar, ta ce rikicin jihar Rakhine na dauke da wasu alamu da ke nuna cewa an aikata kisan kare dangi.
“Da yawa daga cikin ‘yan gudun hijrar sun fuskanci cin zarafi da makusantansu, inda aka kashe musu yara da mazaje a gabansu, aka kuma yi wa matan aure da ‘yayansu fyade ko aka kona su ko kuma aka jikkata su. Wannan duk alamu ne na kisan kare dangi.” Inji Sanata Jeff Merkely na jam’iyar Democrat da ya fito daga jihar Oregon, yayin wani taron manema labarai da aka yi a ofishin jakadancin Amurka da ke Yangon.
Merkely ya fadawa manema labarai cewa, tawagar ta majalisar dokokin Amurka ta nemi gwamnatin Myanmar da ta aiwatar da shawarwarin da kwamitin da Kofi Annan ya jagoranta ya bayar, sannan a kyale Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu su samu hanyar kai wa ga yankin da ake rikici, domin gudanar da ayyukan jin kai.
A nan Washington, Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, na duba yiwuwar saka wannan rikici na Myanmar a matsayin na kare dangi.