Tawagar Kwamitin Tsaro Na MDD Sun Ziyarci Borno

Mathew Rycroft Jakadan Birtaniya a MDD

Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya MDD sun ziyarci jihar Borno, don ganin yadda lamarin tsaro yake da kuma halin da al’ummar da rikicin Boko Haram ya rutsa ke ciki.

Kwamitin mai mutane 14 karkashin jagorancin jakadan Birtaniya, Mathew Rycroft, sun fara ziyarar ta su ne da wani sansanin ‘yan gudun hijira da ake kira Arabic Village, inda suka gana da ‘yan gudun hijirar sansanin.

Haka kuma tawagar ta ziyarci rundunar sojojin Najeriya da ke yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram, inda suka zanta da kwamandan rundunar da wasu manyan jami’an sojan kasar. kafin daga bisani su ziyarci fadar gwamnatin jihar Borno, wanda anan ne ma jagoran tafiyar ya shaidawa gwamnatin jihar cewa ba za a iya kawo karshen ta’addanci ba tare da an magance talauci ba, da samar da ilimi da aikin yi da kuma kare fararen hula, da kare hakkin bil Adama musamman mata.

A cewar Jakada Mathew yace birtaniya ta ware wasu kudade masu yawa don tallafawa ci gaban al’umma da horas da jami’an soja, har ma da samar da abinci da harkokin kiwon lafiya.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya mai da jawabi inda yace ‘yan kungiyar Boko Haram basa wakiltar musulunci, kuma makiyan addinin musulunci ne domin abin da suke aikatawa ‘karara ya sabawa musulunci. Haka kuma Shettima yace ‘yan Boko Haram sun lalata ajujuwa 535 a makarantun fimare da sakandare 38 da kuma wasu manyan makarantu biyu duk a jhar Borno.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

Tawagar Kwamitin Tsaro Na MDD Sun Ziyarci Borno - 3'26"