Kungiyar ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya mata, ta Super Falcons, sun mamaye gasar cin kwallon kafar mata ta Afirka, wadanda suka lashe kofin wasan har sau tara tun alif 1991.
Amma ‘yan wasan na korafi kan karancin albashi, da biya ba a kan lokaci ba, haka kuma ana nuna musu banbanci da takwararsu kungiyar kwallon kafa ta maza.
Kungiyar dai ta lashe kusan duk gasar kwallon Afirka ta mata da ake yi tun alif 1991, inda ta lashe wasanni tara cikin wasanni goma sha daya da aka yi.
Toochukwu Oluehi, mai shekaru 31 itace babbar mai tsaron ragar kungiyar mata ta Najeriya, Super Falcons.
Ta ce “Mune muke kawowa ‘kasa daukaka. Saboda haka, ya kamata su duba kungiyar matan, su kuma yi kokari su mayar da hankali kansu, su bar mayar da hankali kan maza kawai. ‘Yan kungiyar maza suna samun kudi fiye da kungiyar mata.”
Kungiyar matan sunfi dogara da gwamnati wajen samun kudi fiye da kugiyar maza ta Super Eagles, wadanda suka lashe gasar Afirka uku kacal. Maza na samun tallafi daga kamfanoni, kuma anfi zuwa wasanninsu.