Turkiyya da Rasha da Iran sun taimaka wajen shirya tattaunawar ta tsawon kwanaki biyu a Astana tsakanin wakilan gwamnati da kuma na 'yan tawaye, inda a karshe su ka amince cewa za su saka ido kan takaitacciyar tsagaita wuta a Siriya su kuma ba da goyon baya ga kokarin da ake yi na samo mafita a siyasance a wannan tashin hankalin da kasar ke fama da shi.
Yildirim ya ce ya kamata mafitar ta hada da kafa sabuwar gwamnati a Siriya wadda za ta yi tafiya da dukkannin bangarorin.
Wani batu mai sarkakkiya a tattaunawar zaman lafiyar da aka yi ta yi a baya shi ne irin rawar da Shugaba Bashar al-Assad zai taka a sabuwar gwamnatin. 'Yan tawayen na so ya sauka daga mulki, to amma magoya bayansa ciki har da Rasha, na so ya cigaba da mulki.