Tattaunawar Zaman Lafiya a Cyprus Ka Iya Rugujewa - MDD

Espen Barth Eide Mai baiwa Babban Sakataren MDD shawara ta musamman akan kasar Cyprus

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a Cyprus yayi gargadin cewa cece-kuccen da ake yi akan hakar Mai da kuma Iskar Gas zai iya jawo roshewar tattaunawar da ake yi ta neman hade kan kasashen yankin.

Espen Barth Eide ya fada jiya Alhamis a Nicosia “barin wannan abu ya lalace sakamakon wannan cece-kuccen zai zama wani abin bakin ciki a wajen mu baki daya.”

Turkiya ta bukaci Girka ta Cypriot da ta dakatar da hakar man da kuma Iskar Gas a tekun Mediterranean har sai an sami yarjejeniyar daidaiton mulki da Yan Cypriots bangaren Turkiya.

Shugaban Cyprus Nicos Anastasiades ya fada a jiya Alhamis cewa “Barazanar” Turkiya ba zatayi aikiba. Inda ya zargi Turkiya da kokarin ruguza tattaunawar da ake akan zaman lafiyar.

An raba Cyprus gida biyu tsakanin Cyprus yankin Girka da Kuma Cyprus Yankin Turkiya a Arewa tun 1974, yayin da dakarun Turkiya suka mamaye kasar bayan Juyin mulkin soji wanda akai kokarin hade Tsibirin da Girka.