Rahoton da ministan ya bayar ya nuna cewa kasar ta samu cigaba a tattalin arziki inda ta haura sama-sama s cikin kasashe talatin mafi arziki.
Ana sa ran a shekara 2017 zuwa 2020 kasar Najeriya zata shiga cikin jerin kasashen nan ashirin da suka fi bunkasa a sha'anin tattalin arziki a duniya. Wannan tsarin tun lokacin marigayi Umaru 'Yar'Addu'a ake binsa domin tabbatar da cewa kasar ta fita daga cikin kangin talauci da lalacin da ake fama da shi.
A firar da wakilin Muryar Amurka yayi da Labaran Maku ministan yada labaran kasar Najeriya yace bai kamata a dinga la'akari da irin talaucin dake cikin kasar ba a yanzu inda wasu ma suna cewa cigaban kasar a tattalin arziki akan takarda ne kawai yake. Ministan yace yaran da ake dauka aiki yanzu sai karuwa su keyi. Yace fatara ba zata kare yau ba sai dai idan gwamnonin jihohi sun hada kai da karfin gwiwa su tabbatar da habakar tattalin arziki a jihohi. Yace gwamnatin tarayya taimako ta ke ba jihohi.
To amma wasu 'yan Najeriya basu yadda da ikirarin da gwamnati ke yi ba domin talauci ya yiwa yawancin 'yan kasar katutu. Ikirarin gwamnatin tarayya tamkar raina hankalin 'yan Najeriya ne.
Ga cikakken rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5