A dai dai lokacin da kasar Iran ta sha alwashin daukar fansar harin da Amurka ta kai ta sama, da ya hallaka babban kwamandan zaratan sojojin juyin juya hali na Iran, Qassem Soleimani, manazarta na ganin zai iya shafar dukkan yankin gabas ta tsakiya, da ma wasu kasashen duniya.
Farfesa Bello Muhammad Bada, malami a jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sokoto, kuma mai sharhi akan al’amura, ya bayyana yadda lamarin zai shafi kasashen Africa musamman Najeriya mai arzikin man fetur, a bangaren tattalin arziki.
A cewar Farfesa Bello, Najeriya ta dade ba ta samu kudin shiga ba kamar wanda ta samu lokacin yakin Iraqi, saboda haka ake ganin idan wani tashin hankali ya faru tabbas farashin mai zai tashi, inda kasashen da ke fitar da Mai irin su Najeriya zasu kara samun kudin shiga.
Sai dai a bangare guda kuma, bayan karin kudin shigar da Najeriya za ta samu, za ta sayo tataccen mai wanda sai ta biya sama da abin da take biya a baya.
Domin karin bayani saurari cikakkiyar tattaunawar da Farfesa Bello Muhammad Bada.
Your browser doesn’t support HTML5