TASKARVOA: Hutun Haihuwa Na Kwanaki 14 Ga Iyaye Maza Da Ke Aikin Gwamnati A Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

A Najeriya, kwanan nan ne gwamnatin kasar ta amince da hutun kwanaki 14 na haihuwa ga iyaye maza da ke aikin gwamnati. Wannan dai hutu ne domin su samu damar shakuwa da jariran su. A watan Yunin 2018, gwamnatin ta kara hutun haihuwa ga iyaye mata daga watanni uku zuwa hudu. Ga fassarar rahoton Gilbert Tamba daga Abuja.