TASKAR VOA: Yadda 'Yan Najeriya Ke Kokawa Kan Karin Farashin Man Fetur

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan karin farashin man fetur a kasar, wanda kawo yanzu ya sanya farashin sauran kaya kara tashi a kasuwanni. Karin farashin man fetur daga Naira 568 da 617 zuwa Naira 850 da 1,400, ya sa kudin mota ya rubanya a wasu wurare, yayin da kayan abinci su ma suka daga.