TASKAR VOA: Duba Akan Bankado Cin Hanci Da Rashawa A Kasashen Afirka Kashi Na Biyu
Your browser doesn’t support HTML5
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce kashi saba’in cikin dari na matsalar zarmiyar kudi da almundahana a kasar, a bangaren hada-hadar banki ake aikata su. A kowacce shekara, dubban ‘yan Najeriya su na kai rahoton almundahana ga hukumomi.