Tasirin Ziyarar Shugaban Facebook Zuwa Najeriya Ga 'Yan Arewa

Usman I. Usman

Hamshakin Matashin nan kuma mamallakin shafin sadarwan nan na zamani wato facebook, Mark Zuckerberg yace yana da fata na gari ga matasan Najeriya masu kirkire kirkire anan gaba.

Mark ya furta hakan ne a lokacin wata ziyarar bazata da yake birnin Legas, a Najeriya, domin gaawa da matasa da ‘yan kasuwa masu hazakar kirkire kirkiren na’urori na fasahar zamani daban daban.

A lokacin wannan ziyara dai Zuckerberg, ya gana da masu kirkire kirkire a cibiyar bunkasa dabarun zamani ta C.C Hope da ke birnin Legas. Usman Ibrahim Usman, daya daga cikin matasa masu fasahar kirkirar man hajar yanar gizo daga Arewa bayyana alfanun wannan ziyarar ta matashin biloniyan ga masu ilimin fasahar yankin Arewaci n kasar.

Yace makasudin zuwansa shine domin a kara bunkasa kafofin bayanai na Najeriya, saboda irin ci gaban da kasar ke samu da kuma ilimin kimiyya na wasu abubuwa da Najeriya ke da shi, da kuma kara bude hanyar ci gaba.

Wannan ziyarar dai ita ce karon farko da mai shafin Facebook matashi Mark Zuckerberg ya kai wata kasa a Nahiyar Afirka.

Your browser doesn’t support HTML5

Shi Kadai Ne Dan Arewacin Najeriya A Ganawa Da Zuckerberg - 3'28"