Sakatariya a ma'aikatar harkokin wajen kasar Kenya, Amina Mohammed tace kasar ta tana samu alfanu sosai daga ziyarar da shugaba Barack Obama na Amirka zai kai kasar.
A wata hira da abokin aikinmu na sashen turancin Vincent Makori yayi da ita jiya Alhamis Amina Mohammed tace ziyarar da shugaba Barack Obama na Amirka zi kai kasar ta tamkar haske ne akan kasar ta kuma gwamnatin shugaba Uhuru Kenyatta.
Tace tana ganin wannan ziyarar da zai kai yanzu yin na’am ne ko kuma amincewa da salon shugabancin da ake da shi. Haka kuma yana nuni da yadda aka fahimci irin nasararon da kasar Kenya ta samu cikin yan shekarun da suka shige.
A lokacinda shugaba Kenyatta da mataimakinsa William Ruto suke fuskantar caje cajen zargin cewa sun da hannu a tarzomar data biyo bayan zaben shugaban kasar da aka yi a shekara ta dubu biyu da bakwai, dangantaka tsakanin Amirka da Kenya ta raunana. To amma akwai alamar cewa wannan ta kau.
Yau Juma’a din nan ake sa ran shugaba Obama zai isa kasar Kenya domin shima ya halarci taron kolin harkokin cinikaya da za’a yi. A yayida shugabanin ‘yan kasuwa daga duk fadin duniya zasu halarci wannan taro Amina Mohammed tana fatar ganin an samu kamfanoni sun zuba sabbin jarurruka a Kenya.
Tace komai na baiyana kuma a yadda al’amurra suke suna fatar kamfanonin zasu yi sha’awar zuba jarurruka a Kenya. Tace yanzu hankali duniya ya koma kan kasar Kenya domin shugaban amirka zai kai ziyara kasar. Tace tana tsamanin kowa na sha’awar sanin abubuwan da suke kasar da kuma abubuwan da kasar zata yi tayin gabatarwa
Baya ga batun harkokin kasuwanci, wani baban batu dake kan ajanda a lokacin ziyarar shugaba Obama shine matsayin batun tsaro. Kasar Kenya wadda ke makwaptaka da kasar Somaliya, yan yaki sa kai kungiyar Al Shabab da cibiyar ta ke kasar Somaliya ta sha auna kasar Kenya wajen kai hare hare. Amina Mohammed tace Amirka ta ci gaba da kasancewa kawar Kenya sosai wajen yaki da ta’adanci.
Tace hadin kai ko kuma tuntubar juna tsakanin kasashen biyu musamman akan matakan tsaro yana da tarihi, domin an dade ana yi. Kodayake a cikin yan shekaru da suka shige an kara kaimin tuntunbar juna a saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a duk fadin duniya.
Haka kuma kasar Kenya tana taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani a rikice rikice a yankin, ciki harda rikicin da ake yi a kasar Burundi a saboda niyar shugaban kasar na sake yin wani wa’adin mulki. Har yanzu dai kasar ta Burundi tana kidayan kuri’un da aka kada a zaben da aka yi a ranar Talata kuma Malam Amina Mohammed tace shugabanin yankin suna nazarin au suyi na’am da sakamakon zaben ko kuma a’a.
Your browser doesn’t support HTML5