Tasirin Wayar Salalu A Najeriya

wata tana amfani da wayar salula wajen huldar banki

Hukumar kula da Kamfanonin sadarwa ta Najeriya wato NCC ta ce 'yan kasar fiye da miliyan 160 suka mallaki layin wayar salula, yayin da sama da miliyan 90 ne daga cikin su ke amfani da fasahar sadarwa ta intanet.

Duk da irin yawan mutanen da suka mallaki wayoyin salula, masana a wannan fanni sunce 'yan Najeriya ba sa bada fifiko wajen amfani da kafofin sadarwa na zamani kan al'amuran da zasu bunkasa rayuwar tattalin arzikin su.

A shekara ta 2002 ne aka fara amfani da tsarin wayar salalu ta GSM a Najeriya, bayan da hukumomin kasar suka baiwa 'yan kasuwa damar saka jari a bangaren harkokin sadarwa.

Ko da yake kamfannin sadarwa na gwamnati wato NITEL da karamin kamfanin MTEL da aka kirkira daga jikinsa sun kwanta dama, akwai kafanonin sadarwa 'yan kasuwa kusan guda 7 dake aikin yanzu a Najeriya, kasar da yawan al'umarta suka tasamma miliyan 200

Ga alama dai har yanzu kalilan daga cikin 'yan Najeriya musamman matasa ne ke amfani da wayar salula da abubuwan da ta zo dasu na zamani domin bunkasa tattalin arzikin su na yau da kullum.

Saurari Cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari

Your browser doesn’t support HTML5

Amfanin wayar salula-3:40"